No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafseer

Mutane 13 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan titin Bida zuwa Mokwa a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutum shida daga ciki mata ne da ke kan hanyarsu ta kai ƙawarsu amarya da ta yi aure.

Rahoton ya ce take suka mutu bayan faruwar haɗarin.

Ƙanin ango na cikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Waɗanda suka shaida faruwar lamarin sun ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙauyen Lukoro da Wuya a kan titin Bida zuwa Mokwa a yammacin Juma’a.

KU KUMA KARANTA: Mummunan hatsarin Mota ya ci rayukan mutane 18 a hanyar Kano zuwa Kaduna

Kwamandan hukumar kare hatsari ta Najeriya a Neja, Kumar Tsukwam wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce mutane 13 ne suka mutu.

Ya ce haɗarin ya faru ne “tsakanin wata Toyota Corolla da Nissan ta haya da suka yi gaba da gaba, kuma mutum 13 sun mutu,” in ji Tsukwam.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...