Daga Ibraheem El-Tafseer
Alaƙar diflomasiyya da tattalin arziƙi da kuma tsaro tsakanin ƙasashen Afrika renon Faransa, na daɗa sukurkucewa biyo bayan dakushewar tasirinta a ƙasashen. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen ke ƙoƙarin ƙulla alaƙar tsaro da tattalin arziƙi da China da Turkiya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Amurka.
KU KUMA KARANTA: Amurka ta sake nanata ƙudurinta na tsayawa tsayin daka a fannin tattalin arziƙi da kasuwanci a ƙasashen Afirka.
Jamus, Wolfram Lacher, ya ce, ƙasashen Afirka da dama na neman sabbin abokan hulɗa a fannin tsaro, saboda abin da za su samu daga gare su ya sha bamban da abin da suke samu daga ƙasashe kamar Amurka da Faransa.
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mali suna amfani ne da sojojin haya na Rasha, a wani yunƙuri na kawo ƙarshen hare-haren ta’addanci a yankunansu.