Yayin da azumin watan Ramadan ke karatowa kasar Saudiyya ta haramta wasu abubuwa 8, a cikin watan na bana.
Abubuwan da aka haramta sun hadar da :-
1.Kashe lasifika lokacin sallar a’sham.
2.An Hana yaɗa bidiyon sallar asham da ta tahajjudi a kafafen yaɗa labarai a duk faɗin duniya.
3.An haramtawa masu yin i’itikafi a masallaci har sai an tantancesu.
4.Sanya dokar takaita sallar dare da ake yi lokacin azumi don kowa ya koma gida da wuri.
5.An hana neman taimako ko tallafi a harabar masallaci da wasu keyi don bada buɗa baki.
6.An hana iyaye zuwa masallaci da yara, inda aka buƙaci masu yara su barsu a gida.
7.Daina yin buɗa baki a farfajiyar masallacin Makka da Madina.
8.Bada umarnin kashe lasifika ko Kuma rage sautinta.