Ƙasar Masar ta tsare ɗan jarida bayan da ƙasar Zambiya ta kai rahoto

0
346

Hukumomin Masar sun kama wani ɗan jarida da ya wallafa labarin yana zargin jami’ai da hannu wajen safarar kuɗi da makamai da zinare zuwa ƙasar Zambiya.

Zargin da Karim Asaad ya yi ya biyo bayan kama wani jirgin hayar da jami’an Zambiya suka yi a filin jirgin saman Lusaka.

An ce yana ɗauke da kuɗi sama da dala miliyan 5 (£3.9m) da kuma bindigu, alburusai da fiye da kilogiram 100 na zinare. Takardun waɗanda ake zargin sun fito ne daga wani bincike na Zambiya an zargi wasu sojoji da ‘yan sandan Masar da dama a matsayin waɗanda ake tuhuma.

Ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasar Masar ta ce Mista Asaad shi ne ɗan jarida na 24 da ake tsare da shi a ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar ‘yan jarida a Yobe sun gana da shugaban majalisar jihar

Mista Asaad yana aiki ne da shafin labarai na Matsda2sh.

Abokan aikin Mista Asaad sun zargi jami’an tsaro da cin zarafin matarsa ​​da yaronsa a lokacin da aka kama shi a ranar Asabar.

Leave a Reply