Ƙasar Mali ta dakatar da gidan talbijin na Faransa kan zargin ‘yin ƙarya’
Gwamnatin mulkin soji ta Mali ta dakatar da gidan talbijin na Faransa LCI daga aiki a ƙasar tsawon watanni biyu, inda ta zarge shi da yin “zarge-zarge na ƙarya ” game da rundunar sojin ƙasar da abokansu na Rasha.
“An dakatar da gidan talbijin na LCI television daga watsa labarai na rediyo da talbijin a Mali tsawon watanni biyu” daga ranar 23 ga watan Agusta, a cewar hukumar da ke sanya ido kan kafafen watsa labarai ta Mali a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.
Tun bayan da sojoji suka yin juyin mulki a Mali a 2020 da 2021, suke yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da masu neman ɓallewa daga ƙasar da ke da ƙarfi a arewacin Mali.
Sojojin sun kori Faransa daga ƙasar, sannan suka ƙarfafa alaƙa da ƙasar Rasha, inda sojojin haya na Wagner suke taimaka musu wajen yaƙi da ‘yan ta’adda.
KU KUMA KARANTA: Ƙasar Mali ta yanke hulɗa da Ukraine kan zargin goyon bayan ‘yan ta’adda
A ƙarshen watan Yuli, ‘yan tawaye Abzinawa sun yi wa sojojin Mali da sojojin haya na Rasha kwanton-ɓauna a arewacin ƙasar, inda suka yi iƙirarin kashe mayaƙa 84 na Wagner da sojojin Mali Mali.
A cewar hukumar da ke sanya ido kan kafofin watsa labarai, wani mai sharhi a gidan talbijin na LCI ya yi zarge-zarge masu cike da ƙarya a wani shiri da ake kira “Wagner Decimated in Mali: the Hand of Kyiv”.
Hukumar ta ce shirin na ƙunshe da “kalamai na cin zarafi da ƙarairayi game da rundunar sojojin Mali da abokan haɗin-gwiwarta na Rasha”.
Ranar 4 ga watan Agusta ne ta yanke hulɗa da Ukraine kan zargin goyon bayan ‘yan ta’adda a ƙasar, zargin da mahukunta a Kyiv suka musanta.
Tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki sau biyu a Mali, sun riƙa dakatar da kafofin watsa labaran ƙasashen waje.
Sun dakatar da fitattun kafofin watsa labaran Faransa irin su RFI da France 24 a watan Afrilun 2022, da kuma France 2 a farkon shekarar 2024.
Kazalika ƙasashen Burkina Faso da Nijar, waɗanda su ma suke ƙarƙashin mulkin soji suna matsa lamba kan kafofin watsa labarai.
Burkina Faso ta dakatar da LCI a watan Yunin 2023 bayan wani wakilinta ya bayar da rahotanni game da yanayin tsaron ƙasar, waɗanɗa sojoji suka ƙaryata.