Ƙasar China ta yi alƙawarin ba da dala biliyan 50 ga nahiyar Afirka

0
121
Ƙasar China ta yi alƙawarin ba da dala biliyan 50 ga nahiyar Afirka

Ƙasar China ta yi alƙawarin ba da dala biliyan 50 ga nahiyar Afirka

Shugaban China, Xi Jinping, ya yi alƙawarin ba da tallafin kuɗi na sama da dala biliyan 50 ga ƙasashen Afirka a tsawon shekaru uku masu zuwa, tare da taimakawa wajen samar da ayyukan yi kusan miliyan daya a nahiyar.

”A cikin shekaru uku masu zuwa, gwamnatin China tana son ba da tallafi na kuɗi na Yuan biliyan 360, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 50.7,” kamar yadda Shugaba Xi ya shaida wa shugabannin Afirka a ranar Alhamis a birnin Beijing, inda ya kuma yi alƙawarin samar da ayyukan yi aƙalla miliyan ɗaya ga ‘yan Afirka.

Kusan shugabannin ƙasashen Afrika 50 ne tare da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres suka halarci babban taron China da Afrika a wannan mako, kamar dai yadda kafar yada labarai ta kasar ta bayyana.

Tuni dai har shugabannin na Afirka suka samu gagarumin alƙawarin zurfafa haɗin gwiwa a fannonin ababen more rayuwa da noma da haƙar ma’adinai da kusuwanci da kuma makamashi.

Da yake jawabi ga shugabannin a yayin buɗe taron a birnin Beijing, Shugaba Xi ya yaba da dangantakar da ke tsakanin China da nahiyar a matsayin “lokaci mafi kyau a tarihi”.

”A shirye China take ta zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka a fannin masana’antu da aikin gona da samar da abaɓen more rayuwa da kuma kasuwanci da zuba jari,” in ji shi.

China wadda ke matsayin na biyu a fannin ƙarfin tattalin arziki a duniya, ita ce babbar abokiyar cinikayya a nahiyar Afirka, kuma tana ƙokari samun dimbin albarkatun kasa na nahiyar waɗanda suka hada da ƙarfen kopa da zinari da lithium da sauran wasu ma’adinan da ke da wuyar samu a wasu yankunan.

KU KUMA KARANTA: Taron ƙungiyar AU na nemo hanyar warware matsalolin da ke addabar nahiyar Afirka

Kazalika ta bai wa ƙasashen Afirka rance biliyoyin kudaɗe da suka taimaka wajen gina abaɓen more rayuwa da ake da buƙata a nahiyar.

Baya ga haka China ta haɗa taron haɗin gwiwa na daban da ko wacce kasa inda ta yi alkawarin inganta ƙawancenta a manyan ayyuka kamar samar hanyoyin jiragen kasa da na’urorin hasken wuta na rana.

Bayan tarurrukan da aka gudanar a ranar Laraba, shugaban ƙasar Zambia Hakainde Hichilema ya ce, ƙasarsa ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin samar da wutar lantarki na China ZESCO da kuma kamfanin PowerChina a Beijing don faɗaɗa amfanin na’urar hasken rana a ƙasarsa.

Najeriya da China suma sun ƙulla yarjejeniyar ”haɗin gwiwa” a fannin samar da ababen more rayuwa, ciki har da ”sufuri da tasoshin jiragen ruwa tare da yin cinikayya tsabtacciya .”

Shugaba XI ya yi wa shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan alƙawarin ci gaba da aikin hanyar layin dogo da za ta haɗa kasarta da maƙwabciyarta Zambia.

Aikin zai faɗaɗa hanyoyin sufuri a yankin da ke gabashin nahiyar ta Afirka mai arzikin albarkatun ƙasa.

Kazalika Beijing ta yi wa Zimbabwe alkawarin zurfafa danganta a fannin ”noma da haƙar ma’adinai da sabbin makamashi da kuma samar da hanyoyin sufuri” a cewar sanarwar haɗin gwiwa da ƙasashen biyu suka fitar.

Ƙasar wadda ke yankin kudancin Afirka da Beijing sun amince su ƙulla wata yarjejeniya da za ta ba da damar fitar da ‘ya’yan itatuwan fiya wato avocados na Zimbabwe zuwa China, in ji sanarwar.

Shi kuma shugaban ƙasar Kenya William Ruto ya ce Xi ya yi alkawarin buɗe kasuwannin China ga kayayyakin amfanin gona na ƙasarsa.

Bangarorin biyu sun amince su yi aiki tare wajen faɗaɗa babban hanyar layin dogo na ƙasar wanda aka gina da kuɗi daga bankin Exim na China – wanda ya haɗa Nairobi babban birnin tashar jiragen ruwa na Mombasa.

Shi ma shugaban Kenya Willian Ruto ya ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa da China kan samar da hanyar Rironi-Mau da Malaba, wanda kafar yada labarai Kenya ta ce ana sa ran za a kashe dala biliyan 1.2.

A bara ne, Ruto ya nemi rancen dala biliyan ɗaya daga China tare da neman a sake fasalin bashin bashin da ake bin kasar don a samu damar kammala sauran ayyukan gine-ginen da suka tsaya cak.

A yanzu haka China na bin ƙasar bashin fiye da dala biliyan takwas.

Leave a Reply