Ƙasar China ta soma duba yiwuwar sayar da TikTok reshen Amurka wa Elon Musk

0
13
Ƙasar China ta soma duba yiwuwar sayar da TikTok reshen Amurka wa Elon Musk

Ƙasar China ta soma duba yiwuwar sayar da TikTok reshen Amurka wa Elon Musk

China ta soma duba yiwuwar sayar da TikTok reshen Amurka ga hamshakin attajirin nan Elon Musk don kare manhajar daga yawan dakatar da ayyukanta da ake yi a ƙasar, kamar yadda jaridar Bloomberg ta bayyana a ranar Litinin.

Sai dai wasu majiyoyi da ke da masaniya game da batun sun ce manyan jami’an China sun fi so manhajar ta ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin ikon kamfanin ByteDance Ltd.

A makon jiya ne, Kotun Ƙolin Amurka ta bayyana cewa za ta amince da dokar dakatar da ayyukan TikTok a Amurka a ranar 19 ga watan Janairun nan – kwana ɗaya kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Donald Trump – saboda matsalolin tsaron ƙasa da ke da alaƙa da China.

A cewar jaridar Bloomberg, tuni manyan jami’an China suka fara muhawara game da tsare-tsaren amfani da TikTok a matsayin wani ɓangare na gudanar da muhimmiyar tattauna kan yadda za a yi aiki tare da gwamnatin Trump.

KU KUMA KARANTA: An ci tarar TikTok dala miliyan 10 a kan gasar yin bidiyon da ya jawo mutuwar yara

A ɓangare guda, shafin X na Elon Musk – wanda a baya aka fi sani da Twitter zai karɓi ragamar ayyukan TikTok a Amurka kana zai ci gaba da gudanar da dukkan kasuwancinsa, a cewar rahoton.

Kazalika rahoton ya ce, zuwa yanzu jami’an ba su kai ga cim ma ƙwaƙƙwarar matsaya ba kan wannan tsari.

”Babu tabbaci ko ByteDance na da masaniya game da tattaunawar gwamnatin China ko kuma yiwuwar sanya TikTok da Musk cikin batun.

Kazalika, babu tabbacin cewa Musk da TikTok da kuma ByteDance sun tattauna game da sharuɗɗan yiwuwar yarjejeniyar,” in ji rahoton.

Leave a Reply