Ƙasar Amurka za ta hana wasu ‘yan Ghana bizar shiga ƙasarta
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka a ranar Litinin ta sanar da cewa, Amurka za ta taƙaita ba da bizar shiga ƙasar ga mutanen da Washington ke gani a matsayin barazana ga fannin dimokuraɗiyya a Ghana.
Matakin na zuwa ne gabanin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi a ƙasar da ke yammacin Afirka a ranar 7 ga watan Disamba.
”Yunƙurin taƙaita ba da bizar zai shafi wasu ‘yan Ghana waɗanda ke yin katsalandan a fannin dimokuraɗiyya ba wai ga ‘yan ƙasa baki ɗaya ko kuma gwamnatin Ghana ba”, a cewar wata sanar da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fitar.
A baya dai Ghana ta sha gudanar da zaɓukanta cikin lumana da sahihanci, sai dai a bana ana ci gaba da samun fargaba da kuma yiwuwar koma-baya ta fuskar dimokuraɗiyya a ƙasar sakamakon zarge-zargen rashin bin ƙa’idoji gabanin zaɓen da ke tafe.
KU KUMA KARANTA: Amurka ta zargi China Da yin harshen Damo a Yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine
Zaɓen na watan Disamba zai kasance babban zaɓe karo na tara a jere tun bayan komawar ƙasar tsarin dimokuraɗiyya a shekarar 1992.
A watan da ya gabata ne babbar jam’iyyar adawa ta Ghana, National Democratic Congress (NDC), ta gudanar da zanga-zangar neman a tantance sunayen masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasar.
Ta yi zargin cewa ta gano dubban mutane waɗanda ba su cancanci yin zaɓe ba sannan kuma an cire sunayen wasu masu kaɗa ƙuri’a daga rajistar zaɓe.
Shugaban ƙasar Nana Addo Dankwa Akufo-Addo zai sauka daga mulki a bana bayan wa’adinsa na biyu kuma na ƙarshe na shekaru huɗu.
‘Yan takara 13 ne hukumar zaɓe ta amince da su tsaya takarar zaɓen shugaban ƙasa a Ghana.