Ƙarancin ruwan sama: Shehun Borno ya ce a yi addu’a

2
309

Biyo bayan ƙarancin ruwan sama a Daminar bana ta 2023, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, ya ayyana taron addu’a domin neman taimakon Allah kan ruwan sama.

Don haka Shehu ya buƙaci al’ummar Musulmi da su fito gangamin taron jama’a domin halartar sallar jam’i da za a yi a nan gaba domin neman taimakon Allah domin samun ruwan sama a jihar.

Wata sanarwa da sakataren Shehun, Zannah Umar Ali ya raba wa manema labarai jiya a Maiduguri, ya ce za a gudanar da sallar raka’a biyu na neman ruwan sama a ranar Litinin a dandalin Ramat da ke Maiduguri da misalin ƙarfe 10:00 na safe.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta magance ambaliyar ruwa a Jigawa – Shettima

Sanarwar ta buƙaci al’ummar Musulmi ba tare da la’akari da shekaru, jinsi da matsayi ba da su fito lungu da saƙo domin halartar addu’a don neman rahamar Allah a kan ƙarancin ruwan sama da ake fama da shi.

2 COMMENTS

Leave a Reply