Ƙananan yara da ke gudun hijira a Chadi na fama da cutar yunwa – MSF

0
212

Ƙungiyar likitoci ta duniya, wato Medecins Sans Frontiere ta ce dubban yara ƙanana waɗanda iyayensu suka tsere daga Sudan zuwa Chadi sakamakon rikicin da ake tsakanin rundunar sojin ƙasar da dakarun kai ɗaukin gaggawa na rundunar RSF suna fama da matsanancin matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.

Chadi ce ta sauke adadin  ‘yan gudun hijira mafi yawa daga Sudan, inda yaƙi ya ɓarke a watan Afrilu, ya kuma laƙume ɗimbim rayuka tare da jikkata da dama.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da ‘yan gudun hijira dubu 8 ne suka tsere daga Sudan zuwa Chadi a cikin makon farko na watan Nuwamba kawai.

Tun da faarko ‘yan gudun hijira kusan dubu ɗari 9  ne  suka kwarara  ƙasar Chadi daga Sudan sakamakonn rikici da ake a ƙasar, kuma yanzu adadin ya ƙaru ganin yadda rikicin ya ta’azzara a yankin Darfur.

Leave a Reply