Ɗan Okada ya yiwa mace mai ciki fyaɗe a Benuwe

2
767

Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwe ta tsare wani mutum ɗan shekara 40 a duniya bisa zarginsa da yi wa wata mata mai ciki wata takwas fyaɗe.

Matar mai shekaru 25 (an sakaya sunanta) an ce an yi lalata da ita ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a gundumar Irabi ta ƙaramar hukumar Obi ta jihar ta hanyar wani mutum mai suna Akpo Igwe, wani direban babur da aka fi sani da direban Okada.

Wata majiya mai tushe da ba ta so a ambaci sunan ta, ta ce matar da ta dawo daga kasuwa ta tsayar da direban babur ɗin, domin ya kai ta gida kawai ɗan okada ya karkata zuwa wani daji ya yi wa matar fyaɗe.

Majiyar dangin ta ce, “Lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata da misalin ƙarfe 7:00 na dare a lokacin da matar ke dawowa daga kasuwa.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ɗaure wata mata mai shekaru 57, kan laifin yi wa yaro ɗan shekara 8 fyaɗe

Ta tsayar da wani okada ta yi ciniki da shi ya kai ta gida. “Don haka a hanyarsu ta komawa gida, mutumin okada ya karkata daga babban titin zuwa wani daji da ke kusa, ya riƙe ta, ya yi mata fyaɗe.

“A cikin haka sai matar ta suma, sai mutumin babur ɗin, yana tunanin matar ta mutu, sai ya ja ta ya jefar da ita a bakin kogi inda ta kwanta har washegari.

“Da safe ta farka, ta gano kanta a cikin wani hali. Ba ta iya tsayawa ba don haka kawai ta kwanta tana addu’ar neman taimako”.

Majiyar ta ƙara da cewa iyalan da suka yi ta nemanta cikin dare daga bisani suka same ta kwance a sume a bakin kogin.

“Lokacin da muka same ta a wannan yanayin sai muka garzaya da ita asibiti yayin da kuma aka kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda mafi kusa da aka kama mai laifin,” inji majiyar iyalan.

An miƙa ƙarar zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Makurɗi inda ake tsare da wanda ake zargin.

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda, SP. Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce za a gurfanar da mai laifin a kotu bayan bincike.

2 COMMENTS

Leave a Reply