Ɗalibi ɗaya ya kuɓuta daga cikin ‘yan makarantar da ‘yan bindiga suka sace a Kaduna

0
88

Malama Khadija AbdulRa’uf Kuriga, ɗaya daga cikin iyaye matan da ke cikin ɗimuwar kwashe ɗaliban, ta nuna matuƙar damuwarta kan rashin sanin halin da sauran ɗaliban ke ciki.

Kwana ɗaya da sace ɗalibai 287 a garin Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, ɗaya daga cikin ɗaliban ya kuɓuta.

Sai dai iyayen ɗalibin sun nuna damuwa da irin halin da yake ciki yayin da iyaye mata ke ta kuka kan rashin sanin halin da sauran ɗaliban ke ciki.

A ranar Alhamis ‘yan bindiga suka sace ɗalibai 187 a ɓangaren sakandire da kuma 125 a ɓangaren firamare a garin Kuriga.

Tun da farko ɗalibai 25 sun samu sun gudo sai kuma a ranar Juma’a wani ɗalibin ya gudo cikin wani irin mummunan hali abin da ya ƙara ta da hankalin iyayen yaran.

KU KUMA KARANTA:Mata na fuskantar koma baya a fannonin rayuwa daban-daban – matan Najeriya

Malama Khadija AbdulRa’uf Kuriga ɗaya daga cikin iyaye matan da ke cikin ɗimuwar kwashe ɗaliban, ta nuna matuƙar damuwarta kan rashin sanin halin da sauran ɗaliban ke ciki.

Malam Sani Abdullahi na cikin malaman ɓangaren sakandiren da su ka tsira da ya ce ‘yan-bindigan sun kashe dan-sintiri ɗaya.

Tun a yammacin jiya Alhamis ɗin da aka sace waɗannan ɗalibai, Gwamna Uba Sani na jihar ta Kaduna ya ziyarci garin Kuriga.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto dai babu wani labari daga ɓangaren ‘yan-bindigan da suka auka wa wannan makaranta.

Sai dai rundunar ‘yan-sandan jihar Kaduna ta ce ta riga ta baza jami’anta don ceto waɗannan ɗalibai.

Leave a Reply