Ɓarnar da aka yi a Gaza ta fi muni fiye da ta yaƙin duniya na II na Jamus — Borrell

0
179

Babban jami’in diflomasiyyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce halin da ake ciki a Gaza “mummunan bala’i ne, mai ban tsoro”, inda ɓarnar da aka samu ta fi wacce aka yi wa Jamus muni a yaƙin duniya na biyu.

Martanin da sojojin Isra’ila suka yi kan harin Hamas na ranar 7 ga Oktoba ya haifar da “yawan asarar rayukan fararen hula”, in ji Borrell a jawabin da ya yi a taron ministocin harkokin wajen EU.

Ya ce EU ta kuma firgita da tashe-tashen hankula a Yammacin Kogin Jordan da masu tsattsauran ra’ayi ke yi, ya kuma yi Allah wadai da matakin da gwamnatin Isra’ila ta ɗauka na amincewa da ƙarin wasu gidaje 1,700 a Birnin Kudus, lamarin da Brussels ke ganin ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Leave a Reply