No menu items!

Sample Page Title

Date:

Rundunar ƴan sanda a Jihar Jigawa ta samu nasarar kama wani mutum dan shekara 50, da take zargi da kera makamai a Karamar Hukumar Ringim.

Alfijir Labarai ta rawaito Kakakin rundunar a jihar, mukaddashin sifuritendan ‘yan sanda Lawan Shisu ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis.

A cewar Shisu, sun kama mutumin ne a ranar 16 ga watan da muke ciki.

“Rundunar ’yan sanda da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama wanda muke zargi da ƙera wa ɓata-gari makamai a garin Yandutsen Kawari,” inji Kakakin ’yan sandan.

KU KUMA KARANTA: Sojoji sun damƙe waɗanda ke kai wa Bello Turji makamamai a Zamfara

A binciken da aka gudanar a gidansa, an samu ƙananan bindigu biyu ƙirar gida, da kuma wasu manya biyu.

Shisu ya ce wanda suke zargin, da kansa ya tabbatar musu cewa yana ƙera makamai da dama, kuma sau tari bai san waɗanda yake sayarwa ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...