Ƴan sanda a Bauchi sun bankaɗo bindigogin AK-47 da miliyan 4.5 a maɓoyar masu garkuwa da mutane

0
183

Kwamishinan ƴan sandan jihar Bauchi, Auwal Muhammad, ya bayyana yadda ƴan sanda suka yi nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK 47 guda 2, alburusai masu guda 55 da kuma naira miliyan 4,580,000 daga maɓoyar masu garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Ninigi jihar Bauchi.

 A cikin wani faifan bidiyo da WikkiTimes ta ci karo da shi daga shafin X na gidan Talabijin Africa Independent Television (AIT) Kwamishinan ya ce ”An yi nasarar ƙwato bindigogi ƙirar AK 47 guda 2 da alburusai 55  a wani maɓoyar masu garkuwa da mutane dake ƙaramar hukumar Ninigi jihar Bauchi.”

Faruwar Lamarin ya biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin rundunar ƴan sanda da jami’an tsaro, ƙarkashin jagorancin Ahmed Ali Kwara, a ranar 26 ga watan Disamba da ta gabata.

KU KUMA KARANTA: NDLEA ta bankaɗo ɗakin da ake haɗa sinadaran ƙwayar meth, ta ƙwato fakitin haramtattun ƙwayoyi da dama

Kwamishinan ya ƙara da cewa, “Dabarun Kwantan ɓauna da rundunar ke yiwa masu garkuwa da mutane hakan na haifar da kyakkyawar sakamako.

 Sakamakon wannan jajircewa rundunar ta samu nasarar korar ƴan bindiga, da ma sauran masu aikata miyagun laifuka.

Har wa yau a yankin Ningin rundunar ƴan sandan jihar ta kuma yi nasarar kashe wasu mutane shida da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Leave a Reply