No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun kashe babban basaraken garin Orsu Obodo da ke ƙaramar hukumar Oguta a jihar Imo, Eze Victor Ijioma da kuma wazirin garin Mgbele shi ma a ƙaramar hukumar.

Rahotanni sun ce maharan sun kashe shugabannin gargajiyar ne a hare-hare daban-daban a jiya Alhamis.

‘Yan bindigar da ba a san ko su wanene ba zuwa yanzu sun hallaka babban basaraken ne a motarsa a garin Izombo kuma suka banka masa.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 18 a Benuwe

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani da ya ga yadda abin ya faru wanda bai yarda a bayyana sunansa ba ya ce maharan sun tare basaraken na al’ummar Orsu Obodo a mahaɗar Umuamaka a garin Izombe da ke maƙwabtaka da nasu, inda suka hallaka shi.

Ya ƙara da cewa domin su tabbatar da ya mutu ne suka sanya wa gawarsa a cikin motar wuta.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Henry Okoye ya tabbatar mata da labarin kashe-kashen a yau Juma’a.

Kuma ya ce Kwamishina ‘yan sandan jihar Muhammed Barde ya ƙaddamar da binciken zaƙulo maharan.

Kashe-kashe da ƴan bindiga kan yi a jihar ta Imo sun ƙaru tun bayan zaɓen da aka yi na jihar da kuma na tarayya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

10 COMMENTS

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...