Ƙungiyoyin mata sun nemi a ba su damar samun kujeru masu yawa a majalisun ƙasa da na jihohi

0
343

Ƙungiyoyin mata sun nemi a ba su damar samun kujeru masu yawa a majalisun ƙasa da na jihohi

Daga Shafaatu Dauda Kano

Gamayyar ƙungiyoyin mata ta ƙasa waɗanda suka haɗa da FIDA, WRAPA, da WACOL, sun gabatar da daftarin dokar da ke neman ƙarin kujeru na musamman ga mata a Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai, da kuma majalisun dokokin jihohi.

Daftarin, wanda aka gabatar wa kwamitin sake nazari akan kundin tsarin mulki na Majalisar Dattawa a Kano, na neman a ware kujeru 37 ga mata a majalisar dattawa, guda ɗaya daga kowace jiha da Abuja.

KU KUMA KARANTA: A kawo ƙarshen cin zarafin mata da nuna ƙyama ga ‘yan mata a jihar Nasarawa, daga Fa’izatu Aliyu Doma

Haka kuma, suna neman kujeru 47 a majalisar wakilai da kuma kujeru 3 ga mata a kowace majalisar jiha.

A cewar Dr. Mohamed Mustapha Yahya, wannan yunkuri yana da nufin magance ƙarancin wakilcin mata a siyasa, duba da cewa su ke da kashi 45 zuwa 49 cikin ɗari na masu kada ƙuri’a a lokacin zaɓe.

Habiba Ahmed daga kungiyar WRAPA ta buƙaci gwamnati da ta amince da hakan tare da gyara tsarin zaɓe domin inganta wakilcin mata a harkokin shugabanci.

Leave a Reply