Ƙungiyar ‘yan kasuwa ta shirya addu’o’i na musamman a Yobe

0
138

Daga Ibraheem El-Tafseer

Dubban jama’a ne suka yi ɗafifi a garin Potiskum domin gudanar da taron addu’o’i na musamman na neman taimakon Allah a cikin halin ƙunci da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da hauhawar farashin kayayyaki a faɗin ƙasar nan.

Ƙungiyar ‘yan kasuwa ‘United Marketers Association Potiskum’ (UMAPO) da ke jihar Yobe, ta shirya taron addu’o’i na musamman, a wani yunƙuri na neman agaji kan mawuyacin halin rayuwa da jama’a ke ciki a jihar.

Neptune Prime Hausa ta tattaro cewa, shugaban ƙungiyar Harmonize Traders Association of Nigeria reshen jihar Yobe, kuma shugaban zartarwa na ƙungiyar ‘yan kasuwa da ‘yan kasuwa ta jihar, Alh Nasiru Mato ya ce ya zama wajibi ayi addu’a ta musamman saboda halin ƙunci da wahala da hauhawar farashin kaya, da ake fuskanta a duk faɗin ƙasar.

Alh Mato ya danganta hauhawar farashin kayayyaki da wasu ‘yan kasuwa ke tafkawa, da tashin farashin Dala, da kuma tsadar safarar kayan da ya shafi cire tallafin mai.

KU KUMA KARANTA: Abin da ya sa muka ce za mu rufe kasuwar Potiskum, kuma mu yi zanga-zangar lumana – Shugaban ‘yan kasuwar Potiskum

Alh Mato ya yi ƙira ga ɗaukacin al’ummar Najeriya da su riƙa yin addu’a da kuma neman taimakon mahalicci, maimakon shirya zanga-zangar da za ta ƙara dagula lamarin.

Da yake kokawa kan halin da ake ciki yanzu, Mato ya ce, yawan laifuka ya kai ƙololuwa saboda kowa na cikin tsananin buƙatar samun kuɗi.

A nasa jawabin, babban Shehi kuma Darakta na ‘yan agajin Ɗarika na Annahada Islamic Corps, Shaikh Muktari Waliy ya yi ƙira ga dukkan musulmi da su nemi gafarar Ubangiji da tuba daga wurin Allah.

A yayin da yake yaba wa ƙoƙarin masu gudanar da addu’o’in, Sheikh Waliy, ya yi ƙira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi da su guji aikata duk wani abu na ta’addanci, tare da bin koyarwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama da kuma Alkur’ani mai girma.

Ya bayyana dalilai kamar cin amana, ɓoye kayayyakin abinci, munafunci da fasiƙanci da munanan ayyuka su ne manyan musabbabin wahala.

Taron wanda aka gudanar da Sallah da karatun Alqur’ani ya gudana ƙarƙashin jagorancin Malam Hassan Parsawa.

Malamin ya kuma shawarci masu hannu da shuni da su riƙa bayar da kyauta ga masu rauni da marasa galihu a cikin al’umma.

Bikin wanda ya gudana a filin wasa na makarantar sakandiren Jeka-ka-dawo ta gwamnati ta Potiskum (Government Day), an gabatar da karatun Al-Qur’ani, kyauta ga marasa galihu da marasa gata da kuma taron addu’a na musamman.

Leave a Reply