Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai dake aiki a Kano ta ƙaddamar da shirin walwalar ‘yan jarida
Daga Jameel Lawan Yakasai
Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai, ƙarƙashin Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), reshen Jihar Kano, ta ƙaddamar da wani shirin walwala mai taken “Tea Break” domin ƙarfafa haɗin kai da zumunci a tsakanin membobinta.
An ƙaddamar da shirin, wanda ya ƙunshi dafa shayi, cin tsire da sauran kayan ƙwalan da maƙulashe a wani ƙwarya-ƙwaryan biki na musamman da aka gudanar tare da halartar membobi da baƙi a ofishin ƙungiyar a Kano.
Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamarwar, shugaban ƙungiyar, Murtala Adewale, ya ce an tsara shirin ne domin rage gajiyar da ke tattare da aikin jarida da kuma samar da yanayin da zai ba da damar membobi su huta, su tattauna, su kuma ƙarfafa zumunci bayan wahala da gajiyar aiki.
KU KUMA KARANTA: Kamfanin Jaridar Neptune ya horar da ‘yan jarida sanin makamar aiki a Yobe
“Aikin jarida aiki ne mai wahala sosai. Wannan shiri zai bai wa membobinmu damar hutawa, musayar ra’ayi da kuma gina zumunci tsakanin juna a fannin sana’a da na zamantakewa,” in ji Adewale.
Ya ƙara da cewa shugabancin ƙungiyar na da niyyar ci gaba da wannan tsari, inda shirin Tea Break zai zama hanya ta ƙarfafa haɗin kai, inganta fahimtar juna, da kuma kyautata jin daɗin membobi.









