Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa ta koka kan rushe kasuwar Alaba Rago a Legas

0
295
Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa ta koka kan rushe kasuwar Alaba Rago a Legas
Kasuwar Alaba Rago bayan an rushe ta

Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa ta koka kan rushe kasuwar Alaba Rago a Legas

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta bayyana matuƙar damuwarta dangane da ruguje kasuwar Alaba Rago mai ɗimbim tarihi a jihar Legas.

Inda ta bayyana wannan a matsayin babban rashi ga dubban ƴan Najeriya da rayuwarsu ta dogara da kasuwar.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta rufe wani kamfani a Legas mai samar da jabun kayan kwalliya

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaranta na ƙasa Farfesa Tanko Muhammad Baba.

Kungiyar ta ce rusau ya kawo cikas ga rayuwa da kasuwanci na mutane da dama, lamarin da ya janyo asarar dukiyoyi da koma bayan tattalin arziki.

Leave a Reply