Ƙungiyar NASU da SSANU sun tsunduma yajin aiki

0
58
Ƙungiyar NASU da SSANU sun tsunduma yajin aiki

Ƙungiyar NASU da SSANU sun tsunduma yajin aiki

Ƙungiyoyin Ma’aikatan Jami’o’i, sun tsunduma yajin aiki sakamakon rashin biyan su albashi wata huɗu.

Gamayyar ƙungiyoyin (JAC), waɗanda suka haɗa da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’i (NASU) da Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i na Najeriya (SSANU).

A cikin wata sanarwa da ta aike wa dukkanin shugabannin ƙungiyar da ke jami’o’i da su fara yajin aikin a ranar Lahadi.

Sanarwar, wadda Sakataren NASU, Mista Peters Adeyemi da Shugaban SSANU, Mista Mohammed Ibrahim, suka sanya wa hannu, a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce: “Mun yanke wannan hukunci ne sakamakon dakatar da albashinmu ja wata huɗu.”

KU KUMA KARANTA: JOHESU ta ayyana yajin aikin gargaɗi na kwanaki 7

Duk da cewar Shugaba Bola Tinubu ya amince da biyan kashi 50 na albashin da aka dakatar, amma JAC ta ce babu wanda ya samu ko sisi daka cikinsu.

JAC, ta bayyana cewa ta gargaɗi gwamnati a lokuta daban-daban, amma ba a yi komai kan buƙatarsu ba.

Saboda haka, JAC ta yanke shawarar cewa za a fara yajin aikin ne misalin ƙarfe 12 na daren ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba, 2024.

Ƙungiyar ta ce sai gwamnati ta waiwaye sannan za su janye yajin aikin da za su fara a daren yau.

Leave a Reply