Ƙungiyar likitocin NAHCON ta koka da halartar mata masu juna biyu a Hajjin bana

0
628

Hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa NAHCON ta bayyana damuwa kan yawan mata masu juna biyu da suka ƙi bayyana cewa suna da ciki, a zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin hajjin bana.

Shugaban Ƙungiyar likitocin Najeriya Dakta Usman Galadima ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai ranar Laraba a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Galadima ya ce sai an taimaka wa ɗaya daga cikin mata masu juna biyu ta kwanta, yayin da wasu kuma sai an kai su asibitin mata domin samun kulawar da ta dace.

“Mun ga lokuta daban-daban tun daga zazzaɓin cizon sauro, wanda ya zama ruwan dare gama gari da cututtuka na numfashi na sama, kamar tari, ciwon maƙogwaro da kuma kula da masu fama da rashin lafiya.

KU KUMA KARANTA: Dalilin da ya sa muka bambanta farashin Hajjin bana – NAHCON

“Har ila yau, mun samu wasu matan da suka da juna biyu mai kusan watanni bakwai kuma an shigar da su kuma suka haifi jariri na wata bakwai.

“Muna da waɗanda muka kai asibitin mata da ke Makka a nan domin karɓar magani da kulawar gaggawa.

Hakan ya faru ne duk da ƙiraye-ƙirayen da muke yi na hana mata masu juna biyu shigowa aikin hajji.”

Ya nanata cewa bai dace a ɗabi’a ba a bar mata masu juna biyu su tafi aikin hajji saboda damuwa, haɗari da irin waɗannan matan ke fuskanta, ko kuma gamuwa da su a lokacin motsa jiki.

Shugaban tawagar likitocin ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda wasu alhazai da ke fama da rashin lafiya suka zo ƙasa mai tsarki ba tare da izini ba.

A cewarsa, jami’an tsaron Saudiyya a filayen tashi da sauƙar jiragen sama na ba da damar shiga da irin waɗannan magungunan idan suna cikin kayansu na asali da kuma adadinsu.

Sai dai Malam Galadima ya ce bayanan da suka same shi sun nuna cewa, an kama waɗannan ƙwayoyi ne daga Najeriya ne ba a kowane filin jiragen sama na Saudiyya ba, saboda rashin samun cikakkun bayanai, faɗakarwa da ilmantar da irin waɗannan magunguna, kamar yadda suke da alaƙa da haka.

“Wannan ya fallasa wasu daga cikin majinyatan cikin babban haɗari kuma a ƙarshe, shigar da su asibitocin Saudiyya, saboda wasu daga cikinsu suna da matakan sukari da hawan jini ya kai matakin rikici.”

Ya bayyana cewa, tawagar likitocin ta ƙasa sun fara aiki a Madina tare da kafa asibitoci kusan huɗu a cikin rukunin gidajen alhazai.

“Muna ganin mahajjata tsakanin 150 zuwa 200 a kullum tun bayan kafa asibitocin.

Kuma mun koma Makka tun ranar 28 ga Mayu, kuma ya zuwa yanzu mun kafa ɗakunan shan magani guda uku a Makkah.

“Kuma a Makkah mun shirya samun ɗakunan shan magani har guda bakwai yayin da alhazai suka zo za mu ci gaba da samar da ƙarin asibitocin da suka taru,” in ji shi.

Leave a Reply