Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta kakkaɓo jirgin Isra’ila maras matuƙi

0
158

Ƙungiyar Hezbollah ta ƙasar Lebanon ta ce ta kakkaɓo jirgin Isra’ila maras matuƙi da makami mai linzami a yankin Galilee Panhandle.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar da safe inda ta ce ta harba makamin nata da misalin karfe 1:45 agogon ƙasar, (23:45 agogon GMT).

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta ƙi amincewa da ƙudirin MƊD na tsagaita wuta

Ta bayyana cewa ta hango lokacin da tarwatsatsun sassan jirgin ke faɗawa a yankin Galilee Panhandle.

Har yanzu Isra’ila ba ta fitar da sanarwa domin gasgatawa ko kuma karyata iƙirarin na Hezbollah ba.

Sama da Falasɗinawa 12,000 Isra’ila ta kashe zuwa yanzu, inda sama da 8,300 yara ne da mata, haka kuma ta raunata sama da 30,000.

Leave a Reply