Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta kai ziyarar jajanta wa Maiduguri (Hotuna)

0
111
Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta kai ziyarar jajanta wa Maiduguri (Hotuna)

Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta kai ziyarar jajanta wa Maiduguri (Hotuna)

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ƙarƙashin jagorancin shugabanta, gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq CON, ta isa Maiduguri domin jajanta wa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum da al’ummar jihar kan bala’in ambaliyar ruwa da ake tsaka da fuskantarsa.

A ranar Alhamis suka isa jihar, Gwamna AbdulRazaq da wasu gwamnoni huɗu sun ziyarci Gwamna Zulum a zauren majalisar da ke gidan gwamnati da ke Maiduguri, inda suka jajanta wa gwamnan da al’ummar jihar Borno dangane da ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi.

Sun kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya gafarta wa waɗanda suka rasa rayukansu tare da roƙon Allah Ya baiwa iyalansu ƙarfin halin jure rashin da ba za a iya maye gurbin sa ba.

Da yake bayyana da dalilin ziyarar, Gwamna AbdulRazaq ya ce sun kai ziyarar ne domin tabbatar da goyon bayan gwamnatin jihar Borno tare da isar da saƙonsu ga gwamnatin tarayya domin ƙara bayar da tallafi wanda zai rage raɗaɗin ga waɗanda abin ya shafa.

Gwamna Zulum ya yi farin ciki da zuwan tawagar da Gwamna AbdulRazaq ya jagoranta bisa ziyarar tare da neman taimakon waɗanda abin ya shafa. Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya saka musu da alheri.

Bayan ziyarar gaisuwar, Gwamnan Borno ya zagaya da takwarorinsa (Gwamnoni) domin duba halin da ake ciki da kuma irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi.

KU KUMA KARANTA: Ambaliyar Ruwa: Mutane miliyan 1 sun shiga wani hali – Zulum

Gwamnonin da suke tare da Gwamna AbdulRazaq a ziyarar sun haɗa da Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, Gwamnan Jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa, da Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni.

Da suka zagaya wuraren da lamarin ya faru, gwamnonin sun shaida yadda ambaliyar ta lalata gidaje, kasuwanci, da ababen more rayuwa. Sun kuma ga mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon haka da kuma al’ummomi da dama da abin ya shafa.

Ziyarar da shugaban NGF ya jagoranta ta nuna goyon baya ga gwamnatin jiha da mutanen kirki. Ziyarar ta kuma nuna ƙauna da haɗin kai da goyon bayan da ake samu a ƙungiyar gwamnonin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Gwamna AbdulRazaq na jihar Kwara.

Leave a Reply