Ƙungiyar ƙwadago ta buƙaci gwamnati ta biya ma’aikata 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

0
75

Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa ta NLC tare da TUC ta ‘yan kasuwa, sun nemi gwamnati ta biya 615,000 ga ko wane ma’aikaci a matsayin mafi ƙarancin albashi, sai dai wasu na ganin abu ne mai wuya idan an yi la’akari da zunzurutun bashin da ake bin Najeriya, wasu kuma suna ganin yaudara ce kawai.

Ƙungiyoyin sun tabbatar da cewa sun aike wa kwamitin da mataimakin Shugaban ƙasa ya naɗa domin duba yadda za a inganta albashin ma’aikata ba tare da tayar da jijiyoyin wuya ba.

Kwamred Nasir Kabir, shugaban tsare-tsare na ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, ya ce mafi ƙarancin albashin (₦615,000) shi ne abin da suka amince da shi, kuma a kansa za su tsaya, babu gudu babu ja da baya.

Nasir ya ce inda a ra’ayinsa ne, abin da ya kamata a biya ko wanne ma’aikaci ya zama aƙalla Naira miliyan ɗaya duk wata.

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar NLC ta gudanar da zanga-zanga, saboda tsadar rayuwa a faɗin Najeriya

Amma wata ma’aikaciya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce wannan ba abu ne mai yiwuwa ba, domin ko albashin dubu sha takwas da gwamnatin baya ta ce a biya ma’aikata har yanzu wasu jihohi ba su biya ba, balle kuma ƙarin dubu talatin da gwamnatin baya ta yi. In an ce a ɗaga zuwa dubu ɗari shida har da goma sha biyar, wa zai iya biya? Wannan yaudara ce kawai.

Yusha’u Aliyu ƙwararre a fannin tattalin arziƙi, ya ce ba lallai ba ne gwamnati ta amince da wannan buƙata, domin za ta auna yawan ma’aikata da ta ke da su da kuma yawan kuɗin shiga da ta ke samu kafin ta amince. Saboda haka abu ne da zai zama sai an duba da idanun basira, domin a yanzu haka gwamnatin tana da basussuka da dama a kanta.

Ya zuwa yau dai ana bin gwamnatin Najeriya bashin akalla Naira Triliyan 87.9, kuma tuni har ofishin ƙididdiga ya fito da ƙiyasin cewa yawan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 33.20 a watan Maris ɗin 2024 daga kashi 31.70 cikin 100 a watan Fabrairun 2024.

Leave a Reply