Ƙudan zuma sun kusa hana sallar jumu’a a Potiskum

1
590

Daga Ibraheem El-Tafseer

A ranar jumu’a (11/08/2023) da ta gabata ne, wasu gungun ƙudan zuma, masu cizo suka tarwatsa taron masu sallar jumu’a a garin Potiskum jihar Yobe. Abin ya faru ne a masallacin jumu’a na cikin sabon gidan Fursuna (New prison) kusa da unguwar Tashar Aduwa a cikin garin Potiskum. Masallacin yana ɓangaren gidajen ma’aikatan gidan fursuna ɗin (staff quaters), mafi yawan masu shigowa sallah ɗin mutanen cikin gari ne.

Wakilinmu ya yi tattaki har zuwa masallacin, inda ya tattauna da wasu daga cikin ma’aikatan gidan fursuna ɗin, Malam Ali M. Ya’u dashi aka yi Sallah lokacin da abin ya faru, ya shaida wa Neptune Hausa cewa “Su waɗannan ƙudan zuma mun san da su tun kafin Azumi, amma da yake ba su taɓa tashi irin wannan ba, sai ba a ɗauki wani mataki akansu ba. Amma jifa-jifa suna cizon mutane, amma ba kamar yadda suka yi ranar jumu’a ba.

KU KUMA KARANTA: Wasu iyaye sun kashe ɗansu saboda gudun nan gaba ɗan zai koma ga Aljani

An alaƙanta fitowarsu da yawa a ranar jumu’a ɗin da jin ƙamshin turare, wanda aka fesa a masallacin domin masallacin ya yi ƙamshi. Jin wannan ƙamshin turare ya sa suka fito da yawa suka tarwatsa waɗanda suka zo sallah. Masallata da yawa sun gudu, wanda hakan ya tilasta dole ba a yi sallah a farfajiyar masallacin ba, kamar yadda aka saba. Waɗanda suke cikin harabar masallacin, sune aka kulle su, suka yi sallah a ciki. Sauran jama’a kuma daga nesa da masallacin suka bi sallar”

Malam Muhammadu Gabdan, shi ne babban limamin masallacin, ya shaida wa wakilinmu cewa “ina gida na shirya zan tafi masallacin, sai ga ‘yan agaji sun zo suka ce Malam kar ka je masallaci a yau, domin ƙudan zuma sun fito suna ta cizon mutane. Sai nace ai ni kuwa dole na je masallacin. Haka na rufe kaina da abaya ta, na shiga masallacin. Na ƙwanƙwasa aka buɗe na shiga muka yi sallah a daidai lokacin da muka saba yin sallah, wato 2:00 na rana.

Ƙudan zuman sun ciji mutane da yawa, hakan ya sa aka yi ta gudu ana barin masallacin. Sun ciji wani dattijo mai larurar ciwon ƙafa (ba ya iya tafiya) mai suna Alhaji Adamu, da ƙyar ‘yan agaji suka fita da shi. Sai da aka masa allurai har da ƙarin ruwa sannan ya farfaɗo. Wuni ya yi yana amai, amma yanzu jikin da sauƙi” inji Liman.

Ma’aikatan gidan fursunan, sun shaida wa Neptune Hausa cewa “mun aika an nemo mana masu cire ƙudan zuma ɗin, wasu masu cirewar sun zo daga garin Gadaka sun duba, sun ce za su dawo daga baya su cire su daga masallacin. Zuwa haɗa wannan rahoton dai an dawo sallah lokuta biyar kamar yadda aka saba a kullum.

1 COMMENT

Leave a Reply