Ƙasurgumin ɗan ta’addan da ya addabi mutane a arewa, ya miƙa wuya ga sojojin Najeriya

0
308

Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa wani ƙasurgumin kwamandan ƙungiyar ta’addanci na Boko Haram, mai suna Bulama Bukar, ya miƙa wuya ga dakarunta a yankin Gubio, jihar Borno.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da darakta labarai na rundunar soji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya saki a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba, a Abuja.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa ɗan ta’addan da ya miƙa wuya ya kasance kwamandan sansanin Boko Haram a Tapkin Chad da ke ƙauyen Gilima a ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Ya ƙara da cewar, kayayyakin da aka samo daga ɗan ta’addan da ya miƙa wuya sun haɗa da bindigar AK 47 guda ɗaya, makamai 5, harsasai 7.62 guda 44, wuƙa ɗaya, babur ɗaya da kuɗi Naira 23,500.

“A yanzu haka, ana ɗaukar bayanan ɗan ta’addan.”

A halin da ake ciki, kakakin rundunar sojin ya ce dakarun soji na nan suna aikin buɗe wuta domin raba ƙasar da tsagerun ‘yan ta’adda, masu tayar da ƙayar baya da sauran miyagu a faɗin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Rashin tsugunar da ‘yan Boko Haram da suka miƙa wuya babban haɗari ne- Barista Bulama Bukarti

Mista Nwachukwu ya ce a kan haka ne dakarun bataliya ta 2 suka kai kwantan ɓauna kan wasu ‘yan ta’adda a yankin Udawa dake ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna a ranar 17 ga watan Oktoba sannan suka sheƙe ‘yan ta’adda uku.

Ya ce wutan da aka buɗe masu ya sa sauran sun tsere, yayin da sojojin suka ƙwato wata bindiga ɗauke da harsashi 111, babura biyu, babban rediyon sadarwa mai ƙarfin gaske da kuma wayoyi guda biyu.

A cewarsa, wani soja ya rasa ransa a yayin arangamar, rahoton Leadership.

Ya ƙara da cewar a wannan ranar, dakarun Birgediya ta 1 sun kama wani da ake zargin yana kai alburusai a ƙaramar hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.

Ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa wanda ake zargin yana hanyar kai wa wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Gishiri harsashi ne.

A cewarsa, dakarun ‘yan banga sun ƙwato wata jaka ɗauke da harsashin 7.62mm guda 224, wayar hannu ɗaya da kuma kuɗi naira 4,000 daga hannunsa.

Leave a Reply