No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ƙasar Libya ta musanta shirin sayar da ɗanyen mai ga kamfanin Ɗangote

Kamfanin mai na ƙasar Libya (NOC) ya musanta zargin ƙulla wata yarjejeniya ta samar da ɗanyen mai ga matatar mai ta Ɗangote a Najeriya.

NOC ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a shafinsa na X, yana mai mayar da martani bisa ga iƙirarin da wani babban jami’i a kamfanin Ɗangote ya yi cewa ƙasar Libya na ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar samar da ganga 650,000 ta ɗanyen mai a kowace rana ga matatarsu.

”Kamfanin mai na ƙasa ya musanta batun ƙulla wata tattaunawa kan samar da ɗanyen mai da wata matatar mai a Najeriya,” in ji sanarwar NOC.

Kazalika kamfanin ya ce, ya himmatu wajen mutunta yarjejeniya da takwarorinsa na ƙasashen duniya sannan yana ”bin dokoki da tsarin sayar da ɗanyen mai na ƙasar Libya kana ba ya ya yarda ya karkatar da alƙiblarsa zuwa wani wuri.”

KU KUMA KARANTA: Kalaman wasu jami’an gwamnatin Najeriya kan matatar man Ɗangote tamkar kwancewa ƙasar zani a kasuwa ne – Masana

Libya tana fitar da ɗanyen mai da ya kai ganga miliyan 1.28 a kowace rana, a cewar NOC.

Wannan bayani ya haifar da ruɗani a kasuwannin man fetur na duniya, la’akari da hasashen manazarta kan cewa yarjejeniyar ka iya yin tasiri wajen ƙara farashin mai da kuma samunsa a kasuwanni.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...