No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ƙasar Ivory Coast ta umarci sojojin Faransa su fice daga ƙasar

Sojojin Faransa za su fice daga ƙasar Ivory Coast a watan nan na Janairu, a cewar shugaban ƙasar Alassane Ouattara a wani jawabi na ƙarshen shekara da ya yi wa ‘yan ƙasar ranar Talata.

Mista Ouattara ya ce ya ɗauki matakin ne da zummar zamanantar da dakarun ƙasarsa.

Ya ce, “Lokaci ya yi da za mu yi alfahari da sojojinmu, waɗanda suke aiki bisa ƙwarewa. Don haka mun yanke shawarar janye dakarun Faransa daga Cote d’Ivoire cikin lumana.”

Shugaban na Ivory Coast ya ce yanzu sojojin ƙasarsa za su maye gurbin na Faransa a Bataliya ta 43 ta Sojojin Ruwa a Port Bouet da ke kudancin Abidjan inda dakarun Faransa suka yi sansani.

Faransa tana da dakaru fiye da 600 a ƙasar Ivory Coast waɗanda ta jibge domin yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin.

Ivory Coast ta bi sahun ƙasashen Mali, Burkina Faso, Nijar da Chadi, waɗanda suka kori dakarun Faransa daga cikinsu bayan sun zarge su da hannu wajen tayar da rikice-rikice.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Faransa ta janye jiragen yaƙinta daga Chadi

Hakan na nuna yadda ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka suke ci gaba da yi mata bore, lamarin da ya rage tasirinta a nahiyar Afirka.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...