No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin ƙasar Chadi ta bai wa wasu ma’aikatan diflomasiyya huɗu na Sudan wa’adin awa 72 su fita daga ƙasar sakamakon wasu “kalamai masu nauyi” da jami’an Sudan suka yi cewa Chadi na rura wutar rikicin Sudan.

Ma’aikatan diflomasiyyar sun haɗa da babban jami’in diflomasiyya a ofishin jakadancin Sudan da ke Chadi, da babban jami’in tsaron ofishin da kuma ma’aikata biyu, kamar yadda gwamnatin Chadi ta bayyana ranar Asabar.

An ɗauki matakin ne bayan wani babban jami’in sojin Sudan Janar Yassir al-Attaya ya yi “kalamai masu nauyi marasa dalili,” sannan shi ma ministan harkokin wajen Sudan ya maimaita su a wani gidan talbijin, in ji sanarwar da kakakin gwamnatin Chadi ya fitar.

“Waɗannan kalamai da jami’in gwamnatin Sudan suka yi a kan Chadi da gwamnatin kasarmu ba abu ne da za mu amince da shi ba , kuma suna tunzura jama’a sannan cike suke da wata kullalliya,” a cewar sanarwar.

Kawo yanzu gwamnatin Sudan ba ta ce uffan game da korar da Chadi, wadda ke makwabtaka da ita, ta yi wa jami’anta ba.

KU KUMA KARANTA: Ƙananan yara da ke gudun hijira a Chadi na fama da cutar yunwa – MSF

Yaƙi ya ɓarke a Sudan tun watan Afrilu tsakanin dakarun sojin ƙasar da na rundunar Rapid Support Forces (RSF) lamarin da ya yi sanadin kisan dubban mutane, sannan miliyoyi suka tsere daga gidajensu, ciki har da dubbai da suka tsallaka cikin Chadi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...