Zamfara: NUJ Ta Buƙaci Malaman Addini Da Kiyaye Furucinsu Lokacin Ramadan

2
557

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), ta buƙaci mazauna Jihar Zamfara da malaman addinin Islama da su guji furta kalaman batanci da za su iya tunzura Jama’a, iya kawo wani cikas da zai iya haifar da rashin kwanciyar hankali a bisa irin zaman lafiya da ake da shi a yankin na Arewa maso Yamma.

Sakataren kungiyar NUJ na shiyyar ‘A’, Kwamared Abdulrazak Bello ne ya yi wannan roko a wajen taron lacca na Ramadan na shekarar 2022 wanda kungiyar NUJ reshen Jihar Zamfara ta shirya.

Ya ce “Wannan waki’ar da aka gudanar, ta zo a daidai lokaci ya dace kuma tana da matukar muhimmanci idan aka yi la’akari da manufarta, wato ta mayar da manyan malamanmu kan muhimmancin amfani da kalmomi masu kyau a yayin da suke wa’azi, ba wai kawai a cikin irin wannan watan Azumin na Ramadan ba, face ko kafin da kuma bayan ta watan Azumin.” Inji Shi

A cewar Bello, aikin Jarida na zamani yana nuni ne da a dage da bin diddigin sana’ar ta hanyar gujewa yin aikin jarida na rashin nuna kwarewa, da yin aikin jarida na kiyayya, da nuna kabilanci.

Da yake yabawa kungiyar NUJ sashen Rediyon Zamfara da ta shirya taron da karramawa, magatakardan kungiyar ta NUJ na Shiyyar “A”, ya jaddada kudirinsa na tabbatar da hadin kai, ci gaba al’umma, da ci gaban daukacin ‘yan Jaridu a Jihar, da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya.

“Za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu don mu canza ƙungiyarmu ta kowane fanni, da inganta haɗin kai a tsakanin membobi kuma mu kasance masu kirkira don haɓaka Jihar, Ƙungiyarmu, da mutanenmu kamar yadda zuriyarmu ke jiranmu.” Acewarsa

A karshe, Abdulrazak Bello, ya roki ’yan Jaridu a Jihar Zamfara da su ba da muhimmanci ga kokarin shugabancin NUJ na yanzu a karkashin jagorancin Cif Chris Isiguzo na tabbatar da kwarewa da kuma bunkasa aikin jarida na zamani a fadin kasar nan baki daya.

2 COMMENTS

Leave a Reply