Zaizayar ƙasa na barazana ga mazauna Unguwar Yamma dake Garko a Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Alʼummar Unguwar Yamma da ke Karamar Hukumar Garko a Jihar Kano na neman ɗauki kan barazanar zaizayar kasa da suke fuskanta daga wani ƙaton rami da ke mamayar yankin.
Wannan na cikin wata sanarwa da Comr. Abbas Ibrahim Adam Kwanar Garko ya fitar a madadin masu kishin garin.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Neja ta hana yin bukukuwan babbar Sallah a jihar
Ya ce sun shafe tsawon lokaci suna fama da wannan matsalar da ke ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin mazauna yankin.
“Ga fargaba bisa la’akari da daminar bana, wacce tazo da karfin gaske, muddin mahukunta basu shawu kan wannan lamari ba, gaskiya rayuwarmu da ta iyayenmu da Mazauna wannan yanki na cikin barazana bisa rashin tabbas” a cewar sa.