Za a ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar matan Kannywood ta AKAFA gobe asbar

0
453

A yanzu haka, shirye-shirye sun kammala domin gudanar da taron ƙaddamar da sabuwar ƙungiyar matan Kannywood mai suna ‘Association of Kannywood Female Artistes’ (AKAFA) wanda za a yi a gobe Asabar, 23 ga Yuli, 2022.

Za a yi taron a ɗakin taro na ‘Meenah Events Centre’ da ke Kano.
Shugabar ƙungiyar ta ƙasa, Hajiya Rashida Adamu Abdullahi Maisa’a, ita ce ta sanar da hakan a lokacin tattaunawar da ta yi da mujallar Fim a game da taron.

Hajiya Rashida ta yi bayanin cewa: “A gaskiya, mu a yanzu mun kammala shirin taron, ranar kawai mu ke jira domin gudanar da shi. Kuma wannan taron zai bai wa kowa mamaki, domin mun gayyaci manyan mutane na masana’antar Kannywood da malamai da ‘yan siyasa da sauran jama’a domin su zo su ga abin da ‘yan fim su ke yi na alheri, ba kamar yadda a ke ba su labarin mu ba.

“Domin kuwa mu ‘yan fim mutane ne masu abubuwan alheri, to sai dai ba a faɗa, sai ya zama abin da wasu kaɗan daga cikin mu su ke yi shi ne ya ke zama labari a wajen mutane. To mutane za su zo su ga aikin mu na alheri.”

A game da halartar ‘yan fim a taron kuwa, Rashida ta ce: “Ba mu ɗauke wa duk wata jaruma ba domin taron na duk matan da su ke yin fim ne, tun daga farkon Kannywood har zuwa wannan lokacin. Don haka masu ‘ya’ya da jikoki duk kowa ya zo da su, don taron na sada zumunci ne a tsakanin ‘yan fim da ‘ya’yan su, wanda kuma mu na sa ran abin ya ɗore har zuwa jikokin mu, don ba ma fatan abin ya tsaya a iya kan mu.”

Ta ci gaba da cewa: “Ina tabbatar wa da mutane wannan taron ya bambanta da duk wani taro da aka ta yi a cikin masana’antar Kannywood, domin zan iya faɗa maka cewa ba a taɓa yin taro irin wanda za mu yi ba saboda harkar fim ta mata ce. Don haka a yanzu mun haɗu jaruman mu da furodusas ɗin mu da mawaƙan mu da ma duk wata mace da ta ke yin aiki a cikin masana’antar, mun dunƙule za mu yi tafiya tare domin neman ‘yancin kan mu. 

“Don haka daga yanzu mu na da tsarin da ba za mu rinƙa zama kara-zube ba kamar yadda mu ke yi a baya. Don za mu rinƙa taimakon junan mu; ko mace ba ta da lafiya, ko ta samu kan ta cikin matsala, za mu shiga mu fita domin ganin ta samu ‘yanci.

“Kuma daga ‘yanzu duk jarumar da ta yi aiki aka hana ta kuɗin ta za mu shiga cikin maganar don ganin a karɓar mata haƙƙin ta.”
Daga ƙarshe, shugabar ta ƙungiyar AKAFA ta yi fatan za su yi taron lafiya su gama lafiya.

Leave a Reply