Yau Shekaru 11 da Rasuwar Sarkin Kano Alhaji Dr Ado Bayero
Daga Jameel Lawan Yakasai
A Rana irin ta yau a 6 Ga Watan Yuni shekarar 2014, Sarki Na 13 A Mulkin Fulani Alhaji Ado Bayero ya rasu a fadarsa yana da shekaru 84 a duniya, kuma an yi masa jana’iza a makabartar kakanninsa a Gidan Sarki da ke Nassarawa yayin da dubban al’umma suka fito domin yi masa bankwana ta karshe tare girmamawa.
Ado Bayero da ne ga Abdullahi Bayero, tsohon sarki, wanda ya yi mulki na Tsahon shekaru 27. Ado ya hau karagar mulki ne a ranar 22 ga Oktoba, 1963, inda ya zama sarki na 13 a mulkin Fulani, kuma ya zama sarki na 56 a masarautar Kano. Yana daya daga cikin sarakunan da suka fi dadewa kan karagar mulki a tarihin masarautar. Marigayi Sarkin Kanon ua Shafe Shekaru 51 a Kan Mulki.
KU KUMA KARANTA: Tsohon shugaban ƙasa Umaru ‘Yar’Adua ya cika shekaru 15 da rasuwa
Ya kasance tsohon shugaban jami’ar Ibadan Najeriya har zuwa rasuwarsa.
A ranar 19 ga watan Janairun 2013, wani yunkurin kisan gilla da bai yi nasara ba, ya yi sanadin rasuwar wasu mutanensa biyu da direbansa da mai tsaron lafiyarsa, da dai sauransu.
Alhaji Ado Bayero tsohon ma’aikacin banki ne kuma ya yi aikin dan sanda. Ya kuma taba zama dan majalisar dokoki sannan kuma tsohon jami’in diplomasiya.