‘Yansanda sun gurfanar da matashin da ya haye kan allon talla a Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Rundunar ’Yansandan Jihar Kano ta gurfanar da matashin nan da ya haye kan allon talla yana barazanar faɗowa.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda a Kano za su yi binkice kan matashin da ya hau ƙarfen tallace-tallace
Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an gurfanar da matashin a gaban Kotun Majistare Mai Lamba 5 da ke Gyadi – Gyadi, bisa zargin yunƙurin kashe kansa.