‘Yansanda na neman haɗin kan al’umma don ci gaba da samun zaman lafiya a Kano
Daga Jameel Lawan Yakasai
Rundunar ‘YanSanda ta Jihar Kano ta sanar da wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a ranar Lahadi, 25 ga Mayu, 2025, misalin karfe 8:15 na dare, a karamar hukumar Rano, inda bisa koke-koken jama’a, wani mai gyaran babur da ake kira Abdullahi Musa (namiji), wanda ake zargi da kasancewa cikin yanayin maye, aka kama shi bisa tuhumar yin tukin babur cikin hatsari da rashin kwarewa. An tsare shi a ofishin ‘yan sanda, daga bisani kuma ya fara nuna alamun rashin lafiya, lamarin da ya sa aka garzaya da shi Asibitin Gwamnati na Rano, inda ya rasu a safiyar yau Litinin, 26 ga Mayu, 2025, misalin karfe 6:00 na safe, yayin da yake karbar magani.
Biyo bayan wannan lamari, wasu bata-gari sun kai hari ofishin ‘yan sanda na Rano, inda suka wawashe wasu kayayyaki, suka kona wani bangare na ofishin da wasu motoci biyu, suka lalata wasu motoci goma (10) sannan suka jikkata DPO (Shugaban ‘yan sanda na ofishin). DPO din ya rasu a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, inda aka kai shi domin karbar kulawar likitoci.
An kama mutane ashirin da bakwai (27) da ake zargi da hannu a wannan lamari. Yanzu haka an kwantar da tarzoma, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.
READ ALSO:Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matashin da ya kona masallata a Kano
Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Ibrahim Bakori, PhD, bayan ya kai ziyara wajen faruwar lamarin da kuma yin ta’aziyya ga Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Mohammed Isah Umar (Autan Bawo 19), ya bada umarnin a gudanar da cikakken bincike na gaskiya da adalci, domin gano musabbabin wannan lamari da kuma daukar matakin da ya dace akan duk wanda aka samu da laifi.
Rundunar tana jajantawa da iyalan DPO da ya rasa ransa yayin gudanar da aiki, tare da bukatar jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji daukar doka a hannunsu, su kuma baiwa binciken da ake yi cikakken lokaci da goyon baya.
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano na tabbatar da aniyar ta na ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar, tare da bukatar hadin kai daga kowa da kowa domin cimma wannan buri.