‘Yansanda a Katsina sun cafke matar auren da ta kashe kishiyarta a Daura

0
84
'Yansanda a Katsina sun cafke matar auren da ta kashe kishiyarta a Daura

‘Yansanda a Katsina sun cafke matar auren da ta kashe kishiyarta a Daura

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar ‘yansandan jihar Katsina sun tabbatar da cafke wata mata mai suna Rabiya Labaran mai shekaru 23, bisa zargin kashe kishiyarta, Zainab Lawal mai shekaru 30, a unguwar Sabon Gari da ke cikin garin Daura, karamar hukumar Daura jihar Katsina m

Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar, yana mai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na dare a ranar 24 ga Mayu, 2025, bayan da wani rikici ya barke tsakanin matan biyu har ya rikide zuwa tashin hankali.

KU KUMA KARANTA:An kashe mutum 1, da dama sun jikkata a rikicin manoma da makiyaya a Yobe

Rahoton ya ce mijin matan, Nasir Yusuf, ne ya sanar da ‘yan sanda cewa ya dawo daga kasuwa ya iske matarsa ta fari, Zainab, kwance cikin jini a gida bayan an caka mata wuka.

Jami’an ‘yan sanda daga ofishin Sabon Gari karkashin jagorancin DPO sun garzaya wajen da lamarin ya faru, inda suka kai marigayiyar asibitin Federal Medical Centre, Daura, amma likita ya tabbatar da rasuwarta.

Binciken farko ya kai ga cafke Rabi’a Labaran, wadda ke zaune a gidan tare da marigayiyar, kuma ta amsa cewa ita ce ta aikata kisan bayan wata sabani da suka samu da kishiyarta.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu, ya yi kira ga jama’a da su guji rikicin cikin gida da daukar doka a hannu, yana mai jaddada muhimmancin warware sabani ta hanyar bin doka da oda.

Rundunar ta ce bincike na ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken abin da ya faru.

Leave a Reply