‘Yansanda a Kano za su yi binkice kan matashin da ya hau ƙarfen tallace-tallace

0
81
'Yansanda a Kano za su yi binkice kan matashin da ya hau ƙarfen tallace-tallace

‘Yansanda a Kano za su yi binkice kan matashin da ya hau ƙarfen tallace-tallace

Daga Jameel Lawan Yakasai

Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta ceci wani matashi mai suna Ibrahim Abubakar, namiji, ɗan shekara 19 daga Jihar Adamawa, wanda ya hau saman wani allon tallace-tallace da ke gadar Lado a ranar 23 ga Yuni, 2025. Ya yi barazanar fadowa kasa don kashe kansa matukar bai hadu da wani shahararren ɗan TikTok mai suna Abdul BK ba.

Da aka samu rahoton, tawagar ƴan sanda suka garzaya wurin da gaggawa, tare da haɗin guiwa da jami’an hukumar kashe gobara, suka fara aikin ceton. Ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna, an kawo ɗan TikTok ɗin zuwa wurin, kuma bayan Ibrahim ya gamsu da hakan, an ceto shi cikin koshin lafiya. Duk da haka yana cikin rauni sakamakon yunwar da ya sha bayan da ya kwashe sa’o’i ba tare da ya ci komai ba, hakan yasa aka garzaya da shi zuwa Asibitin ƴan sanda da ke Bompai domin kulawar lafiya.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya yaba da ƙwarewar aiki da saurin mayar da martani da jami’an tsaro suka nuna wajen ceton rayuwar matashin.

Ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

KU KUMA KARANTA:Dalilin da ya sa matashi ya hau allon tallace-tallace a Kano

Rundunar tana jaddada kudurinta na kare lafiyar jama’a da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma. Haka kuma, tana amfani da wannan dama wajen gargadi ga jama’a akan guje wa irin wannan yunkuri, domin hakan laifi ne da doka ta haramta.

Hakanan, Rundunar na ƙarfafa gwiwar duk wanda ke fuskantar matsin rayuwa ko damuwa da ya nemi taimako daga hukumomi da kwararru da suka dace.

DSP Hussaini Abdullahi
Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ƴan Sandan Jihar Kano

A madadin Kwamishinan Ƴan Sanda,
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano.

Leave a Reply