‘Yansanda a Jigawa sun kama magidanci ɗan shekara 70 kan zarginsa da kashe ‘yar’uwarsa 

0
62
'Yansanda a Jigawa sun kama magidanci ɗan shekara 70 kan zarginsa da kashe 'yar'uwarsa 

‘Yansanda a Jigawa sun kama magidanci ɗan shekara 70 kan zarginsa da kashe ‘yar’uwarsa

Daga Jameel Lawan Yakasai 

’Yansanda a Jihar Jigawa sun kama wani magidanci Adamu Yakubu, ɗan shekara 70 daga yankin Galadanchi da ke ƙaramar hukumar Dutse, bisa zargin kashe ’yar uwarsa Hannatu Hashimu mai shekaru 45, saboda rikici kan rabon filin gado.

Wannan na cikin sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shi’isu Lawan Adam, ya fitar a Jumu’ar nan.

KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda sun gurfanar da matashin da ya haye kan allon talla a Kano

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne ranar Litinin 1 ga Yuli da misalin ƙarfe 3:30 na yamma, bayan da sabani ya shiga tsakanin mutumin da ’yar uwarsa, wanda ya rikide zuwa fada.

Ana zargin Adamu Yakubu da dukan mamaciyar da sanda a lokacin da faɗa ya kaure a tsakaninsu.

Bayan faruwar lamarin, mamaciyar ta koma gidan mijinta inda ta suma, kuma aka garzaya da ita zuwa Asibitin Gwamnati na Dutse, inda likita ya tabbatar da rasuwarta.

Rundunar ta ce an kama wanda ake zargi tare da kwato sandar da ya yi amfani da ita a matsayin shaida.

Sanarwar ta ce yan sanda na ci gaba da fadada bincike, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da shi gaban kotu.

Leave a Reply