Yan ta’adda sun ƙona Ofishin INEC a Ogun

2
545

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da sanyin safiyar Alhamis, sun ƙona ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta da ke Iyana Mortuary lll a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Manema labarai sun tattaro cewa ‘yan bindigar waɗanda adadinsu ya kai kimanin takwas ne rahotanni suka ce sun zarce katangar, inda suka shiga harabar inda suka banka wa ginin wuta daga baya.

2 COMMENTS

Leave a Reply