‘Yan sanda sun shawo kan matasan da suka fito zanga-zanga bayan kashe wani mai shekara 67

1
295

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta ce an shawo kan matasan da suka fito zanga-zanga tare da girke jami’an tsaro domin samar da zama lafiya a yankin.

Matasa a birnin Bauchi sun fito zanga-zanga a yau Litinin tare da toshe babbar hanyar zuwa jihar bayan kisan wani mutum mai shekara 67 mai suna Adamu Babanta da ke zaune a yankin Yelwa Labura na jihar.

Tun da sanyin safiya da misalin 7, matasan suka yi dirar mikiya a kan babbar hanyar Bauchi -Tafawa Balewa a gaban kwalejin aikin gona, inda suka toshe hanyar tare da kawo cikas wajen wucewar ababen hawa, wanda hakan ya sanya da yawa komawa amfani da wata hanya.

Jaridar Nigeria Tribune ta ruwaito cewa makwabcin mutumin ne mai suna Mohammed Damina Galadiman Dass ya buge shi da motarsa wanda kuma ya kai ga mutuwarsa.

Wani dan uwan mamacin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce ana zargin wanda ya kashe ɗan uwan na sa da yunƙurin yin lalata da wata yarinya mai shekara 18 mai suna Khadija da kuma ta kasance ‘ya ga marigayin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin.

1 COMMENT

Leave a Reply