‘Yan sanda sun kama ƙoƙon kan mutum da bindigogin AK 47 guda 22 a Adamawa

0
466

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, CP S.K. Akande, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta kama bindigogi ƙirar AK47 guda 22 da kuma mutane da ake zargi da laifuka su 909.

Kwamishina ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jimillar mutane 27 da aka kama kwanan nan a hedikwatar ‘yan sanda a ranar Laraba.

Ya ce, daga cikin mutane 909 da aka kama, 845 daga cikinsu an gurfanar da su gaban kuliya.

Bayanai sun nuna cewa an damƙe waɗanda ake zargi da alaƙa da fashi da makami, garkuwa da mutane, kisan kai, fyaɗe, sauran laifukan jima’i da dai sauransu.

KU KUMA KARANTA:Zaɓen 2023: An tsaurara matakan tsaro a ofisoshin INEC

Hakazalika, rundunar ta samu nasarar kwato ƙananan motoci da manyan motoci 15, Babura 25, Bindigogin bogi ƙirar gida 14 da harsashai 326.

Sauran su ne; bindigogi na ƙirar gida 19, da pumping action gun 4, Sai 12 baka da kibiya, fitilar wuta 4, stabilizer (5000w) binaton janareta TIC mai rawaya ne launi, kosan harsashi 22 da babu komai a ciki, harsashi 7, kwalabe/ wuƙaƙe/sauran muggan makamai guda 27, da kuma na’urar wayar hannu guda 68 ,17, da ƙoƙon kan mutum, da Naira miliyan 4,915 da dai sauransu.

A cewarsa, “duk nasarorin da aka samu kawo yanzu ya samo asali ne sakamakon hadin gwiwa da rundunar ‘yan sandan jihar da sauran jami’an tsaro su ke yi a jihar”.

Leave a Reply