Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 40 bisa laifin kashe ƙaramar yarinya

0
509

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun cafke Barnabas Abduneza ɗan shekara 40, mazaunin ƙauyen Kpasham da ke ƙaramar hukumar Demsa (LGA) jihar Adamawa bisa zargin kashe wata ƙaramar yarinya.

Marigayiyar, (an sakaya sunanta) da mahaifiyarta, ana zargin maharin ne ya kai musa hari a ranar 29 ga watan Satumba, 2022 a ƙauyen Kadamti wanda ya yi sanadin mutuwar ƙaramar yarinya tare da raunata mahaifiyar, kamar yadda kakakin SP Sulaiman Nguroje ya bayyana.

“Bayan harin da wata mata da yaronta suka kai a ƙauyen Kadamti da ke ƙaramar hukumar Numan a ranar 29/9/2022 wanda ya yi sanadin mutuwar jaririn tare da raunata mahaifiyar, jami’an ‘yan sanda da ke sashin Numan, Maza. Operation Farauta da nagartattun Samarin unguwa ne suka shiga aiki suka kama daya dangane da laifin.

“Wanda ake zargin, Barnabas Abduneza mai shekaru 40, mazaunin ƙauyen Kpasham, ƙaramar hukumar Demsa, an kama shi ne bayan wani sahihan bayanai masu inganci.

“Bincike ya zuwa yanzu, an gano abin rufe fuska da wasu muggan makamai kamar yadda wanda harin ya rutsa da shi ya bayyana.

“Saboda haka, kwamishinan ‘yan sanda CP SK Akande ya yaba wa jami’in ‘yan sanda na sashin Numan, da jami’an Operation Farauta da mutanen Numan nagari da suka hana irin wadannan mutanen da suke da shakku su kubuta daga kama su.

“Hakazalika ya umarci mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da CID da ya dauki nauyin gudanar da bincike tare da tabbatar da gurfanar da shi tukuru.

“Shugaban ‘yan sandan ya kara tabbatar wa gwamnati da mutanen jihar Adamawa kudurin hukumar na cika aikinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa,” in ji Nguroje.

Leave a Reply