‘Yan sanda sun kama tsohon soja da ya zama ƙasurgumin dan fashi a Zamfara

1
501

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wani ƙasurgumin ɗan fashin daji a kan hanyarsa ta shiga jihar. An kama ɗan fashin mai suna Sa’idu Lawal da bidigar AK-47 guda ɗaya da AK-49 ɗaya da harsasai masu tarin yawa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar SP Mohammed Shehu Anipr ya sanya wa hannu, ta ce ɗan fashin ya yi ƙaurin suna wajen aikata fashi da makami, da garkuwa da mutane, da safarar makamai da sauran laifukan da ke kawo tarnaki ga zaman lafiyar jihar da maƙwabtan jihohi.

KU KALLI BIDIYON ANAN: https://youtu.be/6N45UtPESNM

Sanarwar ta ce rundunarta mai yaƙi da aikata muggan laifuka ne ta kama ɗan Fashin mai shekara 41, wanda tsohon sojan Najeriya ne da ya taɓa aiki da bataliya ta 73 da ke Barikin soji na Janguza a Kano.

Sanarwar ta ci gaba da cewa an kama tsohon sojan ne a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a hanyarsa ta zuwa Zamfara lokacin da jami’an tsaro suka tsare motarsa domin gudanar da bincike, inda kuma nan take aka kama shi bayan samnunsa da waɗannan makamai.

Dan fashin ya ce ya ɗauko makaman ne daga ƙaramar hukumar Loko a jihar Nasarawa zuwa ga wani Kwastomansa mai suna Dogo Hamza da ke ƙauyen Bacha a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Sa’idu Lawal ya kuma ce ya saba kai irin waɗannan makamai ga kwastomominsa a jihohin Kaduna, da Katsina, da Niger da kuma Jihar Kebbi.

1 COMMENT

Leave a Reply