‘Yan sanda sun kama dillalin ƙwaya a Kano, sun ƙwace tramadol ta naira milyan 25
Daga Shafaatu Dauda Kano
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta ce ta kama wani gawurtaccen dillalin miyagun kwayoyi da aka fi sani da Sulaiman Danwawu, tare da kwace tramadol da kudinsa ya kai kimanin Naira miliyan 25.
An cafke Danwawu ne tare da wasu haramtattun kwayoyi a wani samame da rundunar ta kai, wanda ke daga cikin matakan dakile laifuka a fadin jihar.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a hedkwatar ’yan sanda da ke Bompai, Kano.
Ya ce an kama Danwawu ne duk da cewa an taba cafke shi a shekarar 2022 bisa laifin safarar miyagun kwayoyi.
KU KUMA KARANTA:Rundunar ‘yansanda a Kano ta kama ƙwayar Tramol na sama da Naira Miliyan 150
Kwamishinan ya ce tsakanin 23 ga watan Afrilu zuwa 9 ga watan Mayu, rundunar ta kama mutane 78 da ake zargi da laifuka daban-daban ciki har da fashi da makami, safarar kwayoyi, sata, damfara, da kuma satar dabbobi.
Ya ce sumamen da suka kai ya samu nasara ne bisa hadin gwaiwa da al’umma, bayanan sirri da kuma sintirin awanni 24 da jami’ansa ke yi a sassa daban-daban na jihar.
Daga cikin kayayyakin da aka kwato akwai bindigogi, harsasai, motoci, babura (ciki har da na kafa uku), dabbobi, kwayoyi, kudin jabu da kayan lantarki.
Kwamishina Bakori ya ce akwai nasaba tsakanin safarar kwayoyi da aikata laifuka masu hatsari, yana mai cewa kama masu laifi da kwace kayayyakinsu na daga cikin manyan nasarorin da rundunar ke samu a yunkurin tabbatar da tsaro.
Ya kuma bukaci al’umma su ci gaba da ba da hadin kai da bayar da bayanai masu amfani domin ganin Kano ta ci gaba da zama lafiya.