Yan sanda sun ceto yarinyar da ƙanwar mahaifiyarta ta kulle a Filato

2
543

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta ceto wata yarinya ‘yar shekara 17 da ƙanwar babarta ta kulle a garin Jos babban birnin jihar.

Kamar yadda kamfanin dullancin labarai na Najeriya wato NAN ya ruwaito, cewa jami’ar hukumar kare haƙƙin bil’adama ta ƙasa (NHRC) a jihar Filato, Grace Pam, ta ce an ceto yarinyar ne a unguwar Rikkos da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.

Pam ta ce an kawo yarinyar ne domin ta zauna tare da ƙanwar mahaifiyarta bayan kakarta da ke kula da ita ta fara jinya.

“Hukumar ta samu labari daga wani da yayi ƙorafin da ba a bayyana sunansa ba cewa ’yar uwar ta kulle yarinyar a barandar gidan,” inji ta.

Ta kasance tare da kakarta kafin ta zo gidan innar ta saboda kakar ta yi rashin lafiya kuma ba za ta iya ci gaba da kula da ita ba.

Mai ƙarar ya yi ƙorafin cewa innar ta yi tafiyar kusan mako guda kuma ta bar yarinyar babu abinci.
“Bincike ya nuna cewa lallai yarinyar tana fama da rashin abinci kuma tana da tabo a hannunta, wuyanta, da sauran sassan jikinta.

” Tabon ya samo asali ne daga dukan da ake yi mata ba ƙakƙautawa daga wajen innar.

“An kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda inda aka ɗauki bayanin goggon bayan dawowarta daga tafiyar ta.

“An samar wa yarinyar wurin kwana na wucin gadi har sai ta warke.

“Mun kuma gano cewa yarinyar marainiya ce, ba a taba barin ta fita ba, amma an kulle ta a gida, ba a ba ta abinci ba.

“Ɗaya daga cikin abokan aikinmu ne ya kai ta asibiti don tabbatar da an bata kulawar da ta dace” inji shi.

Shugabar hukumar ta NHCR a jihar Filato ta bayyana damuwarsa kan yadda ake samun yawaitar cin zarafin ƙananan yara, inda ya ƙara da cewa, “a yayin da muke magana, akwai wata yarinya ‘yar shekara tara da ta zo ta zauna da goggonta watanni biyu da suka wuce, da ita ma aka ci zarafinta.

“Dole ne muka kubutar da ita a ranar Alhamis daga hannun innarta; ta yi mata dukan tsiya, amma alhamdulillahi, ba ta samu makanta ba sai dai ta samu rauni a ido”.

Ta ƙara da cewa. “Mun kai ta asibiti a ranar Juma’, ta samu da tabo a jikinta sakamakon duka da aka yi mata.

“Lokacin da ma’aikatanmu suka je wurin, an kulle ta a wani gidan kwano da kwano inda goggon ke ajiye awakinta.

“Yarinyar tana fatan komawa wurin iyayenta.” Inji ta.

2 COMMENTS

Leave a Reply