Yan sanda na binciken cin zarafin budurwa da malamim jami’a yayi, bisa zargin ta ƙwacewa ‘yarsa saurayi

1
729

Yan sanda a jihar Nasarawa na binciken bidiyon wata budurwa da ake zargin wani malamin jami’a ya ci zarafinta bisa zargin tana yunƙurin ƙwace wa ‘yar sa saurayi.

A bidiyon wanda ya karaɗe kafafan sada zumunta an nuno yadda aka ci zarafin budurwar mai shekaru 20 mai suna Blessing Mathias inda ake bugunta aka kuma kekece rigar jikinta da almakashi.

Cikin bidiyon an hasko malamin jami’ar da ke tsangayar koyar da ilimin tarihi na jami’ar tarayya ta garin Lafiya tare da wasu mutane suna cin zarafin Blessing.

Rahotanni sun ce Blessing ta yi yunƙurin ƙwace saurayin ‘yar malamin jami’ar ne bayan da ta faki idonta, ta ɗauki lambarsa a wayarta, lamarin da bai zo wa malamin jami’ar da makusantansa da da daɗiba har ta kai ga sun ɗauki matakin cin zarafinta.

Da yake martani akan bidiyon a kafar tweeter a ranar Asabar, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas Benjamin Hundai ya shaida cewa rundunar’yan sandan jihar Nasarawa na bincike akan lamarin.

1 COMMENT

Leave a Reply