‘Yan sanda a Kano ta kama ƙasurgumin ɗan fashi da makami

0
66
'Yan sanda a Kano ta kama ƙasurgumin ɗan fashi da makami

‘Yan sanda a Kano ta kama ƙasurgumin ɗan fashi da makami

Daga Ali Sanni

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wani ƙasurgumin ɗan fashi da makami tare da ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda biyu da alburusai 47.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, yace sun kuma samu kuɗi kimanin Naira miliyan 4.9 a hannun wanda ake zargin.

A ranar Litinin da misalin ƙarfe 2 na dare ne, wani mazaunin garin Yandadi a ƙaramar hukumar Kunchi da ke Jihar Kano, ya kai rahoton cewa ’yan fashi sun kai masa hari a gidansa, inda suka kwashe masa kuɗi Naira miliyan 15.

Duk da tarzomar da ake fama da ita a Kano sakamakon zanga-zangar yunwa da tsadar rayuwa, kwamishinan ’yan sandan jihar, Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin bin sahun waɗanda suka aikata laifin.

KU KUMA KARANTA: An Kama barayin katin zaɓe 158 a Kano

Da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Talata ne, ‘yan sanda suka kama ƙasurgumin ɗan fashin mai suna Hassan Iliya, mai shekaru 35 mazaunin garin Alhazawa dake  ƙaramar hukumar Musawa ta Jihar Katsina.

Ya shiga hannun rundunar ne yayin da yake ƙoƙarin tserewa a kan babur.

An samu bindigu ƙirar AK-47 guda biyu tare alburusai 47 da kuma kuɗi har N4,986,000.00 a cikin wata jakarsa.

Rundunar ta ce a yanzu haka tana ci gaba da gudanar da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here