Yan bindiga sun sace shugaban Kwalejin Ƙididdiga ta tarayya, tare da wata yarinya a Kaduna

0
435
Armed terrorists. Crowd of military people with weapons. Shooting game airsoft paintball. Military silhouette of soldiers. Army team co workers. Vector illustration

Yan bindiga sun kashe mutun ɗaya, tare da sace Shugaban Kwalejin Ƙididdiga ta tarayya (Federal School of Statistics) da ke garin Manchok a Karamar Hukumar Kaura a Jihar Kaduna.

Wata majiya mai tushe ta shaida wa jaridar Punch cewa an kai hari ne da misalin karfe 8 na dare a ranar Litinin bayan sun yi wa ƙauyen da makarantar tare dirar mikiya.

Majiyar ta bayyana cewa; “Maharan sun kai hari gari ne da dare, inda suka kashe mutum ɗaya, tare da sace Shugaban makarantar da kuma wata budurwa daya.”

Wannan harin na zuwa ne makonni uku bayan sace wasu maka’aikatan lafiya waɗanda suke aikin rabon gidan sauro a garin Zangang-Zankan a Ƙaramar Hukumar Kajuru.

Wani mazaunin garin, John Auta ya faɗa wa majiyar tamu cewa ’yan bindigar da suka auka wa garin sun je da muggan makamai, inda suka riƙa harbe-harben kan mai uwa da wabi.

Ya bayyana cewa mutanen garin sun shaidi irin waɗannan hare-haren daga wajen ’yan bindiga. Ya yi zargin cewa jami’an tsaro ba su yi abin da ya dace domin taka wa abin birki.

Auta ya yi kira ga gwamnati ta tabbatar jami’an tsaro sun ɗauki matakan da suka dace don kawo karshen ayyukan ’yan bindiga da sauran ɓata gari a yankin.

Har ya zuwa haɗa wannan rahoton, ‘yan bindigar ba su tuntuɓi iyalan waɗanda suka sace ɗin ba.
Duk ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin jami’n hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, abin ya ci tura. 

Leave a Reply