Yan Arewa su Shiryawa Ambaliyar Ruwa_ACF
Daga shafaatu Dauda Kano
Ƙungiyar tuntuɓa ta arewa ACF ta yi kira ga gwamnati a matakai daban daban da kuma sauran ƴan ƙasa da su fara shirin fuskantar ambaliyar daminar bana.
Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a matsayin martani kan hasashen ambaliya ta shekarar 2025 da hukumar kula da yanayi ta fitar, inda a ciki hukumar ta lissafa garuruwa aƙalla 1,249 a ƙananan hukumomi 176 da ke jihohi 30, ciki har da jihohi 16 na arewa da cewa za su fuskanci ambaliyar.
KU KUMA KARANTA:MƊD ta saki dala miliyan 5 a cikin shirye-shiryen ambaliyar ruwa, amsa gaggawa a Najeriya
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na hukumar, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ƙungiyar ta nuna damuwarta kan yiwuwar samun yawaitar ambaliyar, da fargabar yadda za ta jawo tsaiko a harkokin rayuwa da walwalar al’umma yankin.
Ƙungiyar ta ce ta ga ƙoƙarin gwamnatin tarayya na wayar da kan al’umma kan batun ambaliyar, amma ta ce ƙoƙarin bai fito fili sosai ba, musamman a yanzu da damina ta fara kankama.